A unguwar Oshodi dake cikin birnin Legas wani rikici ya barke tsamanin 'yan kwamishon tashar mota na yankin inda ake hada-hada kullum.
Rikicin yayi sanadiyar mutuwar mutum daya. Rikicin ya samo asali ne a lokacin da kowane bangaren 'yan kwamishon ya ja daga cewa shi ne yake da hakin karbar kudi a wurin fasinjojin dake zirga-zirga zuwa wasu sassan birnin da ma wasu garuruwan. Lamarin ya kaiga bata kashi tsakanin bagarorin 'yan kwamishon din.
Tuni kwamishanan 'yansandan jihar Legas ya kai ziyara tashar domin gane ma ido nai halin da ake ciki. Ya kuma jirge jamai'an 'yansanda saboda tabbatar da doka da oda.
Matasan da suka yi gumurzu sun yi anfani da makamai kamar su adduna da bindigogi, kulake , kwalabe da dai sauransu.
Wani ganao ya yiwa Muryar Amurka karin bayani. Bayan rikicin duk direbobin sun kwashe motocinsu. Shi ma kakakin 'yansandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin. Yace mutum daya ya mutu. Wasu sun ji rauni. Kawo yanzu sun cafke mutane 19 kana sun samu adduna takwas da harsashai hudu. 'Yansandan na cigaba da kokarin dawo da doka da oda a unguwar.
Ga rahoton Hasan Umaru Tambuwal.
Your browser doesn’t support HTML5