Rikici Ya Barke Tsakanin Jam'iyar APC A Jihar Adamawa

Hotunan zaben 2019

Jami'iyar APC a jihar Adamawa taki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa a jihar da ya bayyana dan takarar PDP Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe kuru'u masu yawa a jihar, lamarin da ya haddasa rikici tsakanin shugabannin APC a jihar ta Adamawa.

Bayan da jam'iyar APC ta sha kashi a jihar Adamawa a zabukan da aka gudanar ta kuma rasa wasu kujerunta na wakilai da kuma na dattawa, yanzu haka an fara zargin wasu kusoshin jam'iyar da cin amana, musamman shugabancin jam'iyar na jihar, zargin da shugabanin na APC ke karyatawa.

Dr Mahmud Halilu Ahmad, daya daga cikin 'yan kwamitin kamfen Buhari yace su basu yi mamaki ba, domin a cewar sa daman sun dade suna zargin akwai masu zagon kasa a cikin shugabanin jam'iyar ta APC, da hakan ya yi sanadiyar fadiwar jami'iyar.

To sai dai shima gwamnan jihar, Senata Muhammad Bindow Umaru Jibrilla,ta bakin kwamishinan yada labaran jihar Ahmad Sajoh ,yace ba haka zancen yake ba.

To ko gaskiya ne cewa da hannun shugabanin jam'iyar a fadiwar da APCn ta yi, Ahmad Lawal shine sakataren tsare tsare na jam'iyar APC a Adamawa ya mana karin haske.

Yanzu dai lokaci ne kawai ke iya tabbatar da yadda zata kaya a zaben gwaman da na yan majalisar dokokin jihar dake tafe.

Saurari rahoton Ibrahim Abdul'Aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Rikici Ya Barke Tsakanin Jam'iyar APC a Jihar Adamawa