Gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al Makura da tsohon gwamman jihar, Sanata Abdullahi Adamu, sun lashe kujerun sanata a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, a cewar hukumar zaben jihar ta INEC.
Jami’in tattara kuri’u a hukumar ta INEC, Farfesa Muhammad Kida ne ya bayyana sakamakon zaben.
Al Makura ya samu kuri’u 113, 156 karkashin jam’iyyar APC a mazabar shiyyar kudancin jihar, wanda hakan ya ba shi damar kayar da abokin hamayyarsa, Suleman Adokwe na PDP, wanda ya samu kuri’u 104,595.
“Alhaji Al Makura Umaru Tanko na jam’iyyar APC, wanda ya cika duk ka’idojin da doka ta tanada, sannan ya samu kuri’u masu rinjaye, ya zama wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.” Inji Kida.
Sannan a daya bangaren kuma, hukumar ta INEC ta ayyana Sanata Abdullahi Adamu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Sanata na shiyyar yammcin jihar ta Nasarawa.
Adamu ya samu kuri’u 115, 298, inda ya doke abokin hamayyarsa Bala Ahmad na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 85,615.
A can jihar Pilato kuwa, jami’in tattara sakamakon zaben jihar a hukumar zaben ta INEC, Farfesa Richard Anande, ya bayyana cewa sakamakon zaben shugaban kasar da aka tattaro daga kananan hukumomi 17, sun nuna cewa, jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 548,665 yayin da APC ta samu 468, 555.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji daga Jos: