Lamarin ya auku ne a yankin Rafin Bauna inda ‘yan kabilar Irigwe ke aikin hakar kuza yayin da Fulani ke gudanar da kiwo a yankin.
Mataimakin shugaban kungiyar raya al’ummar Irigwe Basarake Awezedoro ya shaida cewa yara biyu sun fito daga inda suke aikin kusa inda aka kai musu hari, har biyu suka ransu daya kuma na kwance a asibiti. Awezedoro ya koka da yadda ake kashe musu yara kullu yaumin da kuma rashin daukar mataki ta bangaren gwamnati.
Shugaban Kungiyar Miyetti Allah, Umar Bakare ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin, inda ya kara da cewa an kashe shanu 31 an yanka 8, an kuma nemi 100 an rasa. Bakare ya kuma yi kira ga gwamnati ta hada Fulani da Irigwe wuri daya domin a samu zaman lafiya a yankin.
Jami’an wanzar da zaman lafiya sun ce basu samu cikakken bayani kan aukuwar lamarin ba.
Ga Zainab Babaji da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5