Rick Machar Yayi Maganar Da Ka Iya Sake Haifar Da Rigima A Sudan Ta Kudu

Tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu, Rick Machar, yayi kira akan al’ummar kasar da su tashi tsaye su yi jayayya da shugaban kasar, Salva Kiir – maganar da ake jin tsoron tana iya haifarda rigimar da zata sake jefa kasar a cikin wani sabon yakin basasa.

Machar yayi wannan kiran ne a karshen makon da muka baro bayan wani taron da jam’iyyarsa ta SPLM-IO tayi a birnin Khartoum.

Tun cikin watan Agustar 2014 shugabannin siyasar guda biyu na Sudan ta Kudu sukarattaba hannu akan yarjejeniyar sulhu da juna amma aiwatar da ita ya gagara, karshenta suka watsar da ita baki daya.

Wani babbar kusar jam’iyyar SPLM-IO, Stephen Par Kuol, yace wannan kiran na madugunsu (na cewa a tasarwa gwamnatin shugaba Kiir tsaye) ya biyo bayan hare-haren da gwamnatin da ta dade tana kaiwa ne akan SPLM-IO.

A nasu bangaren, Wek Ateny dake magana da yawun gwamnatin shugaba Salva Kiir, yace Machar mutum ne dake son azzaza rigima da yake-yake, wanda kuma bai tanadar wa mutanen Sudan ta Kudu komai ba.

Ateny yace gwamnatin Salva Kiir ta yanke shawarar cewa ba zata sake komawa fagen daga da sunan yaki ba.