Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ya Nitsar da Gonakin Shinkafa A Nijar


Ambaliyar ruwa a Yamai
Ambaliyar ruwa a Yamai

Mahukuntar kasar Mali sun fitar da sanarwar bude hanyoyin madatsan ruwan kasar domin kaucewa ambaliyar ruwa a kasarsu kuma sun gargadi kasashe kamar Nijar su dauki matakan kariya

To saidai tun kafin wannan gargadin daga Mali wasu wuraren dake gabar teku a Nijar sun samu ambaliyar ruwa inda wasu gonakin shinkafa suka nitse yayinda ruwa ya mamayesu.

Wasu kungiyoyin dake zaman kansu da gwamnatin Nijar sun fara yunkurin karfafa wani babban shamaki tsakanin kogi da wasu unguwannin birnin Yamai kodayake tuni ruwan ya fara mamaye wasu wurare bayan ya nitsar da wasu gonakin shinkafa.

Ministan ayyukan jinkai na Nijar Lawal Magaji dake ziyartar yankin da abun ya shafa yace mutanen dake zaune a bakin ruwa ko wuraren da ruwa ke ci su hanzarta su kaura zuwa inda za'a kebe masu. Yace sun samu labarin ruwan ya fi karfin Mali kuma yana kwararowa zuwa Nijar. Bugu da kari ruwan sama ya kara dagula lamarin.

Gonakin shinkafa da ruwa ya soma mamayewa a yankin Yamai
Gonakin shinkafa da ruwa ya soma mamayewa a yankin Yamai

Sai dai abun ban tausayi shi ne manoma shinkafa da suka soma murmurewa daga barnar da ambaliyar ruwa ya haddasa masu a shekarar 2012 sai kuma gashi bana sun soma hasarar gonakinsu.

Ambaliyar ruwan zata shafi manoma da manyan 'yan kasuwa dake basu kudi su yi noma.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG