Kungiyar ba da agajin gaggawa ta Red Cross, ta ce ta tura wata tawaga biyu ta masu ba da agajin gaggawa zuwa garin Beira mai tashar jirage a Mozambique, don taimakawa dubban mutane da mahaukaciyar guguwar nan mai hade da ruwa ta shafa a makon daya gabata wacce aka yi wa lakabi da Idai.
Wannan guguwa, ta kasance daya daga cikin bala’i mafi muni da ya fadawa yankin kudancin Afirka cikin gwamman shekaru.
Ana sa ran daya daga cikin tawagogin, za ta samar da kayayyakin tsabtace muhalli ga mutum dubu 20,000, yayin da ake sa ran daya tawagar za ta rika samar da tsabtataccen ruwa da yawansa ya kai lita dubu 225,000 a kullum, wanda zai rika taimakawa mutum dubu 15,000 da suke kokarin tsira daga wannan mummunar ambaliyar da ta biyo bayan guguwar.
Wata sanarwa da shugabar kungiyar ta Red Cross a Mozambique Jamie LeSueur ta fitar, ta nuna cewa masu ayyukan agaji sun fi damuwa barkewar cututtuakan da akan samu daga ruwa, tana mai fatan matakan gaggawa da aka dauka, za su dakile aukuwar hakan.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kididdigar adadin mutanen da suka mutu, wadanda ta samu daga gwamnatocin kasashen da bala’in ya shafa, sun nuna cewa a Mozambique mutum 242 suka mutu, a Zimbabwe mutum 139 da kuma Malawi mutum 56.