Red Cross Ta Ce An Kashe Mutane Akalla 187 A Baga

Wani mutumin da ya kone ana kula da shi a bayan fadan da aka gwabza a Baga, Jihar Borno, lahadi 21 Afrilu, 2013

Amurka ta ce tilas gwamnatin Najeriya ta saurari koke-koken zahiri na al'ummar Arewa domin shawo kan wutar irin wannan fitina.
An kashe mutane da dama a lokacin wani kazamin fadan da aka gwabza tsakanin masu kishin Islama da dakarun tsaron gwamnatin Najeriya a yankin arewacin kasar.

Kungiyar agajin Red Cross ta Najeriya ta fada yau litinin cewa mutane akalla 187 ne su7ka mutu a wannan fadan, yayin da ake jinya ma wasu su 77.

Amma kuma, wani kakakin rundunar sojoji a Jihar Borno yace an yi karin gishiri a rahotannin yawan wadanda suka mutu din.

An fara gwabza wannan fada ranar jumma’a da daddare a garin Baga dake bakin tabkin Chadi, abinda ya tilasta ma dubban wannan gari da ya shahara wajen kamun kifi tserewa cikin jeji.

Mutanen garin na Baga sun ce an goce da fada a lokacin da sojoji suka kewaye wani masallacin da aka yi zargin cewa ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram sun buya a ciki.

An yi musanyar wuta sosai, inda aka ce ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun yi amfani da muggan makamai ciki har da gurnetin da ake cillawa da roka. Sojoji da kuma jami’an yankin sun ce ‘yan kungiyar sun yi amfani da fararen hula a matsayin garkuwa, yayin da mazauna garin suka ce da gangan sojoji suka yi ta cinna wuta a gine-gine lokacin wannan harin.

Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Patrick Ventrell, ya fada yau litinin cewa Amurka tana goyon bayan kokarin gwamnatin Najeriya na hukumta masu zub da jini, amma kuma yace tilas ne ta mutunta hakkin jama’a, kuma tilas ta takali koke-koken mutanen arewacin Najeriya.

Yace, "Martaninmu shi ne ba matakan tsaro ne kawai zasu iya murkushe tsageranci ba. Kungiyar Boko Haram tana fakewa da koke-koken zahiri na mutanen arewacin Najeriya wajen neman magoya baya tare da samun tausayawar jama’a. Saboda haka abinda za a yi shi ne a takali wasu daga cikin bukatu da kuma damuwa na zahiri na al’ummar arewacin Najeriya ta yadda kungiyar ba zata iya fakewa da su ba."