Kungiyar bada agaji ta Red Crescent dake Falasdinu tace harin da Isra'ila ta kai ta sama kan wata makaranta a Gaza ya hallaka mutane 28 a yau Alhamis, yayin da rundunar sojin Isra'ila ta bada rahoton cewar harin ya afka ne kan wata cibiyar mayakan Hamas.
Tawagogin jami'an bada agajin Red Crescent sun gano gawawwaki 28 da mutane 54 da aka jikkata sakamakon harin da sojin Isra'ila suka kai kan makarantar Rafida," a cewar kungiyar dake nufin wata makaranta a yankin Deir el-Balah.
Ma'aikatar lafiyar dake karkashin ikon kungiyar Hamas ta wallafa makamancin wannan adadi a sanarwar data fitar
Sanarwar da rundunar Sojin Isra'ila ta fitar tace an kai harin ne a kan mayakan Falasdinawan dake gudanar da al'amuransu a cibiyar "dake boye cikin wani ginin da ake amfani da shi a matsayin makaranta (Rafida).
Sanarwar bata bayyana adadin wadanda suka mutu ba sai dai tace ana amfani da cibiyar "wajen kitsawa tare da kai hare-haren ta'addanci kan sojoji dama kasar Isra'ila."
Harin na yau Alhamis shine na baya-bayan nan a jerin hare-haren Isra'ila ta sama kan ginin makarantu dake baiwa Falasdinawan da suka rasa matsugunansu mafaka a zirin Gaza, inda aka shafe fiye da shekara guda ana gwabza kazamin yaki.
A ranar 26 ga watan Satumbar da ya gabata aka hallaka akalla mutane 15 a wani hari kan makaranta da ta zama mafaka a sansanin 'yan gudun hijirar Jabalia dake arewacin Gaza, a cewar hukumar tsaron farin kaya ta zirin Gaza.