Real Madrid Ta Lashe Kofin La Liga A Karo Na 36

'Yan wasan Madrid suna murna (Photo by OSCAR DEL POZO

Nasarar na zuwa ne bayan da ‘yan wasan Carlo Ancelotti suka lallasa Cadiz da ci 3-0 a ranar Asabar yayin da Barcelona ta sha kaye a hannun Girona da ci 4-2.

Real Madrid ta lashe kofin gasar La Liga a kasar Sifaniya a karo na 36 bayan da ta ba Girona ratar maki 13 a gasar.

Madrid tana da kwantan wasanni hudu a yanzu haka duk da ta lashe kofin.

Nasarar na zuwa ne bayan da ‘yan wasan Carlo Ancelotti suka lallasa Cadiz da ci 3-0 a ranar Asabar yayin da Barcelona ta sha kaye a hannun Girona da ci 4-2.

Da a ce Barcelona ta lashe wasanta da Girona, da Madrid ba ta samu nasarar ba a ranar Asabar.

Girona dai ta dage sai da ta ture Barcelona zuwa matsayi na uku a teburin gasar wacce ke da tazarar maki 14 tsakaninta da Madrid.

A ranar Laraba Madrid za ta karbi bakuncin Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a wasan semi-final.

A karawar farko da Madrid ta bi Bayern gida, an tashi da ci 2-2.