A cigaba da hada hadar 'yan wasan kwallon kafa da akeyi na watan Yuni, shekarar 2019, Real Madrid ta kammala dauko dan wasan Olympique Lyon, mai suna Ferland Mendy.
Mendy ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru shida, wadda za ta kare a karshen kakar 2025. An sayi dan wasan ne kan kudi fam miliyan £47.1,
Real Madrid za ta gabatar da Mendy a gaban magoya bayanta ranar Laraba 19 ga watan Yuni a filin wasa na Santiago Bernabeu.
Itama Manchester United ta kammala sayen dan wasan tawagar kwallon kafa na kasar Wales, Daniel James daga kulob din Swansea City. Dan wasan mai shekara 21 da haihuwa ya sanya hannu kan kwantaragin shekara biyar da yarjejeniyar za a tsawaitata shekara daya, idan ya taka rawar gani a Old Trafford.
Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, John Oblak ya bayyana fatarsa na komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United bayan da mai tsaron ragarta David De Gea shima ya fara shirin barin kungiyar a wannan lokacin.
Rahotanni sun bayyana cewar Oblak yana tunanin cewa kungiyar ba za ta tabuka wani abin kirki ba a kakar wasa mai zuwa saboda duk shekara basa iya cin wani kofi, kuma kungiyar babu wani shiri da takeyi na ganin ta rike manyan ‘yan wasanta.