Rawar Da Matasa Za Su Taka Wajen Gina Tattalin Arzikin Najeriya

Dan takarar gwamna karkashin Jam'iyyar Action Democratic Congress (ADC), a jihar Kano, Salisu Mubarak Muhammad, ya ce, matasa na da kudurori tsararru da za su kai Najeriya ga gaci musamman a fannin gina tattalin arziki.

Yayin da Najeriya ke tunkarar zabe a wata mai zuwa, jami’yyu da dama sun tsayar matasa a gurabe daban-daban domin tsayawa takara.

Hakan ta yi wu ne, tun bayan sanya hannu da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a kudirin dokar ‘Not too young to run,” a watan Mayun bara, wato dokar nan da ta rage adadin shekarun da mutum ya kamata ya kai kafin ya tsaya takara.

A wannan zabe matasa, da suke da kudurori daban-daban, sun fito da kudirunsu na ciyar da Najeriya gaba ta hanyar fito da wasu tsare-tsare a fannin tattalin arziki kamar yadda ake yi a sauran sassan duniya da suka ci gaba, dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar ta ADC ya ce.

A cewar Salisu, matasa ne masu basira da za su iya tunanin hanyoyin ci gaba na zamani, wadanda za su kara da kasashen duniya a fannin kimiya da fasaha, sabanin yadda ake ikrarin cewa iyayen ‘yan siyasa da tunaninsu har kawo yanzu ba ya tafiya da ci gaban duniya.

Salisu, ya bayyana cewa babu kasar da za ta samu ci gaba, ba tare da ta bunkasa fannin tattalin arzikinta ba, ta hanyar amfani da hanyoyin ci gaba na zamani.

Dan takarar na jam’iyyar ta ADC ya kuma yi ikrarin cewa da yawa daga cikin manyan ‘yan siyasar kasar nan ba a shirye suke su ga cewa sun magance matsalar shan kwaya da ta addabi matasa ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Rawar Da Matasa Za Su Taka Wajen Gina Tattalin Arzikin Najeriya 06'34"