Ministan tsaron Najeriya Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya ya ce kalubalen tsaro na haifar da matsalar karancin abinci a sassan kasar.
Janar Magashi ya bayyana hakan ne yayin taron bita da hukumar leken asirin ta rundunar tsaron Najeriya ta shiryawa hafsoshi da ke kula da sha’anin tsaro a ofisoshin jakadancin kasar a kasashen ketare.
Magashi ya kwatanta wannan matsala a matsayin “sabuwar barazana,” lura da yadda take ruruwa, lamarin da ke shafr ayyukan samar da abinci.
Najeriya na fama da aika-aikar ‘yan Boko Haram da ISWAP a gabashin arewacin kasar da kuma ‘yan bindiga dadi da ma rikicin makiyaya da manoma a yammaci da tsakiyar arewacin Najeriyar na haddasa mummunar barazana ga Najeriya a cewarr Janar din mai ritaya.
Kazalika yankin kudancin kasar ma na da nata matsalolin na tsaro da ke shafar ayyukan samar da abinci.
“Yawancin hare-hare da ‘yan ta’adda suke kai wa a kasuwanni ne, saboda anan matattar jama’a take, kuma a nan za su kwashi abinci.
“Bisa wannan dalili ya sa dole ‘yan kasuwarmu da ma su masu sayen kayen suke kauracewa kasuwannin, saboda tsoron a ko da yaushe za a iya far musu.” In ji Alhaji Isa Adamu, mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar arewacin Najeriya.
“Saboda haka, duk lokacin da aka ce ba a bude kasuwanni ba, to dole ne za a samu karancin abinci, kuma duk lokacin da aka samu karancin abinci to dole ne za a samu karin ‘yan ta’addan saboda domin dan adama ba zai iya ruwa bai ci abinci ba.”
A dalilin hakan, ministan tsaron Janar Magashi, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su bullo da dabaru don tunkarar wadannan kalubale.
A cewar masanin tsaro, Salihu Mahmud Dantata, akwai bukatar a mayar da hankali a fannin samar da bayanan tsaro.
“Ya kamata al’uma su zo su rika ba da gudunmowa sannan a arika samun hadin kai tsakanin jami’an tsaro. A kuma samu jirage masu sarrafa kansu don dauko bayanai.” In ji Salihu Mahmud.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5