Rashin Sanin Tarihin Juna Yake Haddasa Rigingimu Tsakanin Al'ummomin Najeriya - Anyaoku

Misalin kayan tarihi da ake ajiyewa

Misalin kayan tarihi da ake ajiyewa

A jawabin da ya gabatar wurin bikin cika shekaru saba'in da kafa dakunan ajiye kayan tarihi a Najeriya, tsohon sakataren kungiyar kasashen renon Ingila Emeka Anyaoku yace rashin sanin tarihin juna ya sa 'yan Najeriya ke fada da juna.

Chief Emeka Anyaoku ya kira shugabannin Najeriya da su koma koyas da daliban kasar tarihin juna saboda a samu cikakkiyar fahimta.

Yayi furucin ne a bikin cika shekaru 70 da kafa gidajen tarihi a Najeriya wanda aka gudanar a Legas. Chief Emeka Anyaoku ya dora laifin rashin fahimtar juna da fadace-fadace da ake fuskanta a kasar da rashin sanin tarihin juna.

Gidajen tarihi gidaje ne da ake ajiye kayan tarihi da ma na al'adun jama'a domin mahimmancinsu a kasashe daban daban. Abun alfahari ne wajen bayyana tarihi da al'adu domin anfanin na baya.

Anyaoku yace saboda haka yana kira ga gwamnatin kasa da ta sake dawowa da koyas da darusan tarihi a makarantunmu bisa ga mahimmancinsa.

Alhaji Yusuf Abdalla Usman babban darakta a gidajen ajiye tarihi yace ma'aikatar ta shekara saba'in bana domin an farata ne a lokacin turawan mulkin mallaka. Kawo yanzu akwai gidajen ajiye tarihi 48 a duka fadin kasar.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rashin Sanin Tarihin Juna Yake Haddasa Rigingimu Tsakanin Al'ummomin Najeriya - Anyaoku - 2' 22"