Taron da aka yi a garin Maiduguri ya mayarda hankali ne akan alakar dake kawai tsakanin cin hanci da rashawa da tsaron kasa.
Jama'a da dama daga sassa daban daban na kasarsuka halarci taron. Sun bayyana irin matsalolin da cin hanci da rashawa ke haifarwa tsakanin al'umma musamman a irin yanayin da ake ciki a arewa maso gabashin kasar.
Shugaban hukumar na jihar Borno Alhaji Yahaya Imam yace sun gudanar da taron ne domin fadakar da jama'a ilolin dake tattare da cin hanci da rashawa musamman a ma'aikatau.
Akan yaki da cin hanci da rashawa hukumar zata yi anfani da jama'a. Zata bi kasuwanni da masallatai da inda mutane ke taruwa kullum domin kowa yana da gudummawar da zai bayar domin a ci nasara.
Son kai na kawo cin hanci da rashawa da kuma rashin godewa Allah da abun da Alla ya bayar. Saboda haka dole a yaki cin hanci da rashawa da malaman addini da na al'umma.
Dr Kamal Dawud masani akan shari'a daga Jami'ar Maiduguri ya gabatar da mukala a taron. Yace kodayake gwamnati ta kuduri yaki da cin hanci da rashawa amma bata dauki matakan da yakamata ta dauka ba. Yace babban alkalin Najeriya ta fada cewa gwamnati bata da cikakkiyar niyar yaki da cin hanci da rashawa. Dokokin kasar basu isa a yi anfani dasu a yaki cin hanci da rashawa ba.
Ga karin bayani.