Kungiyar direbobin kananan motoci ta NURTW ta ce rashin kyawon manyan hanya na taimakawa bata gari wajen satar mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
Shugaban kungiyar Arewa maso yamma Alhaji Alasan Haruna 313, dan asalin Birnin Gwari, ya ce akwai bukatar gwamnati ta gyara hanyar don kawo karshen satar mutane da wasu miyagun ayyuka.
Sai dai kuma shugaban kungiyar hadin kan al'ummar Arewa ta 'Arewa People Unity Association' Alhaji Adamu Aliyu wanda ke cewa ba rashin kyan hanya ne matsalar da ke kawo sace sacen mutane ba.
Maganar tsarkake hanyoyin samar da tsaro sune dai har yanzu damuwar al'umma, a sassan Arewacin Najeriya. Saboda yadda ake yawan sace mutane abun yasa wasu ke ganin sai gwamnati ta sake hanyoyin taimako wajen magance wannan matsalar ta tsaro.
Ga rahoton wakilin muryar Amurka Isah Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5