Rashin Kishin Kasa Shi Ne Ke Hana Wakilai Aiwatar Da Hakkin Da Ya Rataya A Wuyarsu - Shugaban Wata Hukumar Tsaro Mai Zaman Kanta

Kungiya mai sa ido kan ayyukan da ake aiwatarwa a Najeriya - BUDGIT

Ayyukan mazabu da 'yan majalisu ke aiwatarwa a shiyyoyin da suke wakilta, su na yin su ne don samar da ci gaban al'umma.

A wani rahoton wata kungiya mai sa ido kan ayyukan da ake aiwatarwa a Najeriya, mai suna BUDGIT, ta gano cewa tun shekara ta dubu da tara da tasa'in da tara, da aka koma wannan zango na dimokradiyya, gwamnatocin Najeriya ke sakin biliyoyin naira don gudanar da ayyuka a mazabu daban-daban a fadin kasar, duk da shike akan kammala wasu, sau da dama wadansu ayyukan ko dai a fara ba a kammala ba, ko kuma ma ayi sama da fadi da kudadensu.

Mai fashin baki kan lamura, Ahmadu Abubakar Akwanga ya ce cin hanci da rashawa na daga cikin manyan abubuwan da ke sanya rashin aiwatar da ayyuka.

Mafi yawan irin wadannan ayyuka a mazabun siyasa, wakilan al'umma wato sanatoci, 'yan majalisun tarayya da na jaha suke kirkiro su, a wassu lokuta ma, bayanai na nuni da cewa ba su tuntubar al'ummar da zasu amfana da ayyukan kafin aiwatar da su.

Mr Solomon Nandy Chendan, shugaban wata hukumar tsaro mai zaman kanta, Scortbrian Global Security Services ya ce rashin kishin kasa shi ne ke hana wakilai aiwatar da hakkin da ya rataya a wuyansu.

Wadannan lamura na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dattawan Najeriya ke dabaibabaye da bahasin kara a kalla naira tiriliyan hudu da aka cusa kan wasu boyayyun ayyuka a sassa daban-daban na kasar, batun da har ya zuwa yau ,'yan Najeriya ba su fahinci gaskiyar lamarin ba.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Rashin Kishin Kasa Shine Ke Hana Wakilai Aiwatar Da Hakkin Da Ya Rataya A Wuyansu - Shugaban Wata Hukumar Tsaro Mai Zaman Kanta