Da yake jawabi jim kadan bayan zagayen gani da ido game da tashar jirgin ruwa ta kan Tudu a garin Kaduna, ministan sufuri na tarayyar Najeriya Rotimi Amechi ya ce za a kaddamar da wannan tashar tudun ne kawai idan an kammala gina hanyoyi.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jihar da su jira a kammala gina hanyoyin da kuma hauhawar hada- hada a tashar kafin mukaddashin shugaban kasa ko shugaban kasa ya je ya kaddamar da aikin, domin idan babu hanyoyi babu yadda mutane za su iya daukar kayayyakinsu idan an kawo.
Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa’i dake cikin tawagar gani da idon ta ministan harkokin sufurin, ya bayyana cewa akwai riba ainun da gwamnatin jihar Kaduna da kuma al’umar jihar za su iya ci idan aka kaddamar da wannan tashar ta kan tudu a babban birnin jihar.
Ya ce zai ragewa ‘yan kasuwa dawainiyar zuwa Lagos domin dauko kaya.
A cewarsa, dukan abinda mutum zai iya yi a Lagos, zai iya gudanarwa a nan Kaduna, saboda haka wannan zai kawowa ‘yan kasuwar jihohin arewa sauki. Banda haka kuma za a dauki ma’aikata aiki da yawa, wanda yana daya daga cikin muhimman dalilan da yasa gwamnatin jihar ke taimakawa wajen ganin an gama aikin.
Ya bayyana cewa, fiye da kashi 85% cikin dari na al’ummar jihar matasa ne wadanda ba su wuce shekaru 35 ba, wadanda babban abinda suke bukata shine aikin yi.
A nasa bayanin, shugaban hukumar kula da hada hadar jiragen ruwan tarayyar Najeriya Barista Hassan Bello cewa ya yi, duk da yake dai ba a riga an kaddamar da wannan tashar tudu ba, an riga an fara hada-hada.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu Isa Lawal Ikara ya aiko mana daga Kaduna
Your browser doesn’t support HTML5