Tsananin son zuwa kasar Amurka, ya sa na rera wa Amurka waka, kuma na shafe fiye da shekaru 20 ina harkar hip-hop inji Kabiru Abbas wanda aka fi sani da Kano riders.
Ya kara da cewa waka wata aba ce da yake yi domin nusar da al’umma abubuwan da suke faruwa masu kyau da akasin haka domin samar da mafita.
Ya ce yana nishadantarwa, a hannu guda kuma yana ilmantarwa, duk da cewar suna fuskantar wasu kalubalen da suka hada da rashin hadin kai tsakaninsu mawaka inda mafi yawan lokuta sai abubuwa da dama su faru ba tare da an sanar da wasu mawakan ba, wanda ke dakushe masana'antar.
Kabiru riders ya ce lamarin na ci masu tuwo a kwarya sannan babu wani tallafi daga gwamnati da ma wasu kamfanoni, inda yace babban burinsa a yanzu bai wuce ya tsinci kansa a Kasar Amurka ba.
Your browser doesn’t support HTML5