ABUJA, NIGERIA - Wasu daga cikin jigajiganta wadanda sun taba rike mukamai a gwamnatin su ma a yanzu suna ficewa sakamokon abin da suka kira rashin adalci da baza su iya hakuri da shi ba.
Daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC a Najeriya, tsohon ministan matasa da harkokin wasanni Solomon Dalung ya bayyana cewa jam’iyyar ta bijire wa manufofin farko da suka kai ga kafa ta.
Ya kara da cewa Jam’iyyar ta dauki tafarkin jam’iyyar adawa ta PDP wadda tsarinta bai dace da tsarin dimokradiyya ba, da kuma tilastawa ‘yan kasar akan wasu takara, hakan yasa shi bankwana da jam’iyyar ta APC
Masana kimiyyar siyasa a Najeriya dai na alakanta dabi’ar sauye sheka a siyasance da rashin akida ko manufa a siyasa da uwa-uba son kai kamar yadda masanin siyasa Dakta Faruk BB Faruk Shiga ya fada.
Tuni dai shugaban jam’iyyar ta APC Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana bakin ciki game da neman shawo kan ‘yan jam’iyyar musaman daga majalisar dattijai da adadin masu ficewa zuwa wasu jam’iyyu ke dada yawa.
Wadannan kwan-gaba kwan-bayan ne, ya sa ‘yan Najeriya ke ganin yadda manyan ‘yan siyasa ke sauya sheka dama ce ga sauran kananun jam’iyyau sun kai labari a babban zaben kasar dake tafe a shekarar 2023
Saurari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5