Rashford Ya Ba Da Shawarar Yadda Za a Magance Matsalar Cin Zarafi a Kafafen Sada Zumunta

Marcus Rashford, ranar 16 Afrilu 2016. epa/ PETER POWELL

Dan wasan Manchester United wanda har ila yau yake bugawa kasar Ingila kwallo, Marcus Rashford, ya ce magance matsalar cin zarafi a kafafen sada zumunta “abu ne mai sauki.”

Rashford ya kasance daya daga cikin ‘yan wasa da dama da suka fuskanci matsalar nuna wariyar launin fata a kafafen zamani a ‘yan makonnin nan.

Hukumomin kwallon kafa da dama dai sun yi kira ga kamfanonin sada zumunta da su dauki matakan magance nuna wariyar launin fata a shafukansu.

Amma a cewar Rashford, hanya daya da za iya magance wannan matsala ita ce “a rufe shafukan.”

Hukumar kula da wasannin Premier League, FA, EFL, WSL da gasar zakaru ta mata, wato PFA, LMA, PGMOL, duk sun rattaba hannu a wata budaddiyar wasika da aka aikawa shugaban Twitter Jack Dorsey da shugaban Facebook, Mark Zukerberg, inda suka nemi da a dauki matakin gaggawa kan masu cin zarafin mutane a kafafen sada zumunta.

Mutane da dama na ganin gazawar kamfanonin wajen daukan matakan gaggawa idan aka tafka irin wannan ta’asa, inda Rashford ya ba da shawarar cewa kawai a rika rufe shafukan.

“Wannan ita ce hanya daya da za a magance mafi aksarin wannan matsala.” In ji Rashford wanda yake bugawa Manchester United wasa a gaba.