Lavrov yace, al'amrin zai sa Rasha ta sake duba dangantakarta da Turkiyya. Ya soke ziyarar da ya shirya zaikai Ankara jiya Laraban, amma ya zanta da takwaran aikinsa na Turkiyya,kuma sun amince zasu gana cikin kwanaki masu zuwa.
A gefe daya kuma, ma'aikatar harkokin wajen Rashan a cikin wata sanarwa data fitar a jiyan, ta ce ministan harkokin wajen Lavrov a tattaunawar da ya yi da ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ta wayar tarho, ya gaya masa cewa da harbe jirgin saman yakin Rasha, shugabannin Turkiyya sun nuna "suna tareda ISIS."
Ahalinda ake ciki kuma, daya matukin jirgin da Turkiyyan ta harbe wanda yayi amfani da laimar tsira daga cikin jirgin yanzu ya isa wani sansanin sojin Rasha bayan da sojojin Syria suka ceto shi.
A wani lamari kuma, Jami'an tsaron Amurka sun ce suna sa ido kan rahotanni da suke nunin cewa an kai farmaki da jiragen yaki kan wata tawagar motocin ayyukan jinkai jiya Laraba, kusa da da garin Azaz dake Syria, kimanin kilomita shida kudu daga kan iyakar kasar da Turkiyya.