Rasha ta yi harbi kan wadansu jiragen yakin Ukraine guda biyu ta kuma rafkawa na uku a tekun Bahar Asuwad jiya lahadi, suna zargin ‘yan kasar Ukrain da shiga yankin ruwan Rasha ba bisa ka’ida ba.
WASHINGTON D.C. —
Jami’an kasar Ukraine sun ce an jiwa a kalla mayakan ruwa shida rauni, suka kuma musanta aikata ba daidai ba- tare da zargin sojojin Rasha da cin zali.
"daukar wannan matakin yana haifar da barazanar tsaro ga dukan kasashen dake yankin tekun Bahar Asuwad saboda haka akwai bukatar maida martanin kasa da kasa,” inji ma’aikatar harkokin wajen Ukrain.
Ma’aikatar harkokin tsaron kasar Rasha -FSB ta zargi Ukraine da tsokana da gangan.
Cibiyar ta FSB ta fitar da sanarwa dake cewa,”an yi amfani da makamai ne da nufin takawa jiragen yakin Ukraine birki ala-tilas, sabili da haka kuma aka kwace dukan jiragen yakin rundunar mayakan Ukrain uku dake bangaren ruwan Rasha a tekun Bahar Asuwad”