Harin da Rasha da kai Kyiv babban birnin Ukraine da makamai masu linzami da safiyar yau Juma’a ya hallaka akalla mutum guda tare da jikkata wasu 9, a cewar hukumomi.
Moscow tayi ikirarin cewa harin martani ne ga wanda Ukraine din ta kai cikin kasarta da makamai kirar Amurka.
An jiyo karar fashewa mai karfi akalla har sau 3 a birnin Kyiv, jim kadan bayan asubahi.
Rundunar sojin saman Ukraine tace ta kakkabe makamai masu linzami masu cin gajeran zango kirar iskander guda 5 a birnin.
Harin ya lalata tsarin dumama gidaje 630, da asibitoci 16 da makarantu 30 da wuraren renon yara da dama, a cewar hukumar dake kula da birnin, haka kuma burbushin makamai masu linzamin sun haddasa barna tare da tayar da gobara a yankuna 3.