WASHINGTON, DC - A ranar 17 ga watan Yuli ne kasar Rasha ta fice daga yarjejeniyar fitar da hatsi ta tekun Bahar Aswad tsakaninta da Ukraine, da Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya suka taimaka aka cimma, wacce ta ba jiragen ruwa damar shiga da fita tashoshin jiragen ruwa na Ukraine ba tare da an kai musu hari ba. Yayin da miliyoyin mutane a fadin duniya ke fuskantar karancin abinci da ba a taba ganin irinsa ba, wasu na fada wa kangin yunwa. "Ga bil’adama, sakamakon yanke shawarar hana damar samun abinci ga wadanda suka fi bukata a duniya mummunan abu ne," a cewar shugabar Asusun tallafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya USAID Samantha Power.
“Bari mu fayyace nasarorin da shirin fitar da hatsi ta tekun Bahar Aswad ya cimma. Kashi biyu bisa uku na alkama da aka fitar ta hanyar wannan shirin ya tafi kasashe masu tasowa. Kashi 55 cikin 100 na gaba dayan kayayyakin da ake fitar wa ta hanyar shirin sun tafi kasashe marasa karfi. A saboda haka, bayan manoman Ukraine da za su ga sakamakon, mutane a fadin duniya ne za su fi jin jiki saboda wannan hukuncin da Rasha ta yanke,” a cewar Power.
Gaskiyar ita ce, tun da farko bai kamata a ce shirin fitar da hatsi ta Bahar Aswad ya zama da muhimmanci ba. "Dalilin da ya sa ya zama da muhimmanci shi ne saboda Rasha ta mamaye Ukraine sannan ta yanke shawarar toshe tashoshin jiragen ruwa, ta hana Ukraine tura hatsi kasashen duniya," a cewar sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken. "Sakamakon matakin da Rasha ta dauka a yau, inda ta yi amfani da abinci a matsayin makami a yakin da take yi da Ukraine, zai sa a shiga wahalar samun abinci a wuraren da ake matukar bukatarsa."
“Maganar dai a nan ita ce, sam bai dace ba. Bai kamata hakan ya faru ba. Ya kamata a farfado da shirin ba tare da bata lokaci ba. Kuma ina fatan kowace kasa tana sa ido sosai a kan batun. Kasashe za su ga cewa Rasha ce ke da alhakin hana damar samun abinci ga mutanen da ke matukar bukatarsa a duniya, da kuma rawar da ta taka wajen haddasa hauhawar farashin kayayyaki a daidai lokacin da kasashe da yawa ke ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayayyaki sosai,” a cewar Blinken.
"Muna kira ga gwamnatin Rasha da ta gaggauta sauya matakin da ta dauka," a cewar mai kula da harkokin tsaron kasa John Kirby.
Kirby ya ce Amurka na aiki da wasu kasashe don ganin hatsin Rasha da na Ukraine sun kai ga kasashen duniya kuma za ta ci gaba da yi, gami da tabbatar da cewa takunkumin da Amurka ta sanya wa Rasha bai auna abinci da takin kasar ba, sabanin farfagandar da Rasha ke yada wa.
Amurka, a cewar Kirby, "za ta ci gaba da taimaka wa Ukraine a kokarin da take yi na kai hatsi kasuwannin da ke matukar bukatarsa ko da ta wasu hanyoyi ne."