Rasha Da Syria Sun Zargi Amurka Da Yin Karya

Shugaban Syria, Bashar al Assad (Dama) da takwaran aikinsa na Rasha, Vladimir Putin (Dama)

Kasashen Syria da Rasha, sun ce Amurka karya ta ke yi kan zargin da ta yi na cewa an yi amfani da makamai masu guba a yakin basasan da ake yi a Syrian.

Syria da Rasha sun zargi Amurka da yin karya kan batun cewa an yi amfani da makamai masu guba a yakin da ake yi a Syrian.

A fadinsu, Amurka ta yi hakan ne domin neman hanyar kauce wa kokarin da ake yi na ganin an kawo karshen fadan.

Kamfanin dillacin labaran kasar na Syria da ake kira SANA, ya dauko sharhin da ma'aikatar harkokin wajen Syria ta yi inda ta ambaci wannan batu.

Sharhin da SANA ya dakko, ya nuna cewa, karya ne da kazafi kawai sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya yi shi da ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves-LeDrian.

Shi ma mukaddashin Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Ryabkov, ya fadawa kamfanin dillacin labaran Interfax cewa "duk lokaci da aka samu ci gaba ta fuksar zaman lafiya, "sai Amurka ta yada kage da rahotanni marasa tushe."

Wadannan kalaman dai duka suna zuwa ne kwana daya, bayan da Amurka ta bi sahun kawayenta da ke kungiyar tsaro ta NATO, wajen fara nuna matsin lamba ga Syria game da amfani da makamai masu guba a rikicin Syria.

Kungiyar ta NATO, ta tsame Rasha, a matsayin kasar da take marawa Syrian baya da kuma gwamnatin Bashar al- Assad.