Ranar Yaki Da Sa Yara Ayyukan Karfi Ta Duniya

Kananan yara suna aikin karfi

Bayanan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa, miliyoyin kananan yara ne ake tilastawa ayyukan karfi, ko bauta, ko karuwanci, wani lokaci ma harda safarar miyagun kwayoyi domin biyan bukatun iyayensu

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 12 ga watan Yumi a zaman ranar yaaki da bautar da yara kanana. A bana, ana maida hankali ne kan jawo hankalin duniya dandane da harkokin ilimin kanaan yara.

Bayanan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa, miliyoyin kananan yar ane ake tilastawa ayyukan karfi, ko baua, ko karuwanci, wani lokaci ma harda safarar miyagun kwayoyi domin biyan bukatun iyayensu.

Duk da cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka rabbata hannu a kundin kare kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, kanannan yara a kasar suna fuskantar matsala kama daga aikin gida, da barace barace ,da kuma rashin karatu.

Wakilinmu na Lagos Babangida Jibril ya aiko mana da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar Yaki Da Sa Yara Ayyukan Karfi Ta Duniya:2:31