Ranar Tunawa Da Amfanin ‘Kasa A Duniya

Wani manomi Ali Danladi cikin ruwa da ya bata masa gona a kusa da wa ni kauyen Ringim,kusa da Dutse,a jihar Jigawa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar biyar ga watan Disambar kowacce shekara domin tunawa da amfanin ‘kasa a duniya.

Amfanin wannan rana dai shine wayarwa al’umma kai wajen sanin irin muhimmiyar rawar da ‘kasa ke takawa a rayuwar bil Adama.

Wakilin Muryar Amurka a Ibadan Hassan Umaru Tambuwal ya zanta da wasu manoma kan wannan rana, inda ya zanta da Obulu Shagon Danboga, wanda yace ya fara noman Masara da Kubewa da Alayyahu da kuma Yakuwa, sai bashi da masaniya ko ilimin irin kasar da yake shuka a kanta.

Shi kuma Mohammadu Mai Agogo wanda ya kwashe shekaru biyar yana Noma a jahar Oyo, amma bashi da masaniyar wannan rana ta amfanin ‘kasa, amma kuma kasancewar ya dade yana noma yasan ire iren ‘kasa musammanma irin ‘kasar da ta dace wajen noma amfanin gona daban daban.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Umaru Tambuwal.

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar Tunawa Da Amfanin ‘Kasa A Duniya - 3'06"