Ranar 13 ga watan Fabrairu, rana ce da aka ware domin tunawa da irin rawar da kafar sadarwa ta radiyo ke takawa a al’amuran yau da kullum a duk fadin duniya.
WASHINGTON D.C. —
Maksudin kebe wannan rana shi ne a yi amfani da kafar ta radiyo domin kara hadin kan kasashen duniya musamman a tsakanin masu yada labarai.
Baya ga haka an kebe ranar ne domin kara tunatar da gidajen radiyo muhimmancin bayar da dama ga kowa da kowa wajen yin amfani da kafar radiyo domin fadin albarkacin baki ba tare da nuna wariya ga wani saboda jinsi ko addini ko wanin haka ba.
Hukumar da ke kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta saka taken wannan shekara a matsayin ranar da za a yi amfani da radiyo a lokutan kai daukin gaggawa.
Saurari wannan rahoto na Ibrahim Abdulaziz domin jin karin bayani game da wannan rana ta radiyo:
Your browser doesn’t support HTML5