Jihar Adamawa na cikin manyan jihohin da ake noma shinkafa a Najeriya da ka iya wadatar da yankin Arewa maso Gabashin kasar. Manoman na kukan rashin kula da su ne ta fuskar samar da kayayyakin bunkasa bunkasa noma da kuma ban ruwa ga manoman shinkafa dake garin Geriyo wanda yake daya daga manyan guraren da ake noman shinkafa a jihar Adamawa.
Shugaban kungiyar manoma shinkafa na Geriyo Muhammadu Kawu, ya bayyana cewa suna samun karancin ruwa a gonakin su kuma hakan bashi da nasaba da rashin biyan kudin ruwa, hakan na faruwa alokacin da fadama ta kafe wanda kusan duk shekara cikin watan hudu zuwa biyar.
Ya kuma kara da cewa sun sanarwa gwamnati wannan matsala inda aka fara kunna wata na’ura a gefen kogin Benue don taimakawa. Duk da yake su manoman na bukatar a janyo bututu daga kogin zuwa fadamar da take basu ruwa domin kawar da matsalar kafewar ruwan.
Kamar yadda manoman ke kokawa su kuwa hukumomi na nace suna nasu kokari wajen sharewa manoman hawaye. Alhaji Sharif Muhammad wanda yake jami’in kula da harkar noma na Geriyo, ya shaida cewa yanzu haka suna kokarin tayar da injin bakin kogi, domin samarwa da monoman ruwa.
Ga karin bayani.