A duk ranar goma sha daya ga watan Yuli, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a matsayin ranar bukin yawan al’umma a duniya, da nufin samar da tsarin yawan al’umma, don samar da ingantacciyar rayuwa, da kuma zayyana ayyukan daza a samar wa al’ummar.
A dangane da hakane majalisar dinkin duniya ke amfani da wannan ranar, don fadakar da hukumomi da kuma al’umma abubuwan da suka kamata su yi saboda a samu ci gaba da samun al’umma mai albarka a dukkan bangarorin duniya.
Malam Anas Ibrahim, malami a jami’ar jihar Gombe da ke Kashere a jihar Gombe, yayi karin bayani kan muhimmancin wannan ranar da aka shafe kimanin shekaru 32 ana bukin don karrama yawan jama'a a fadin duniya.
Rahotannin na bayyana cewa a lokacin da ake bukin wannan shekarar, ana samun karuwar al’umma a Najeriya, wanda aka danganta da rashin tsarin iyalai, musamman a yan kunan karkara.
Hajiya Maryam Garba, wata jami’ar kungiyar Fahimta mai zaman kanta dake fafutukar inganta rayuwar mata, tayi karin haske a kan wannan ranar da tsarin ta.
A halin da ake ciki yanzu gwamnatocin jihohi tare da hadin gwiwar kungiyoyin fararen hula, sun dukufa wajen fadakar da al’umma ta hanyar ziyarar gidajen al’umma, don ganar dasu fa'idar tsarin iyali.
Malam Ibrahim Yusuf, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin, shima yayi karin haske kan wannan ranar da muhimmancin ta.
Ga rahoto cikin sauti na wakilin muryar Amurka Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5