Ranar 29 Na Watan Gobe Kamfanin Starbucks Zai Rufe Shagunansa Dubu Takwas

Kamfanin Starbucks mai shayin zamani

Hukumomin kamfanin Starbucks mai sayar da shayin zamani ya bada sanarwar rufe shagunansa dubu takwas a duk fadin Amurka domin ma'aikatansa kan illolin nuna wariyar fata wanna ko ya biyo bayan abun kunyan da ya faru a wani shagon kamfanin a birnin Philadelphia inda manajan ya kira 'yan sanda su kama wasu bakake biyu

Shagon sayar da shayin zamani na Starbucks, ya ce a ranar 29 ga watan Mayu, zai rufe shugunansa sama da dubu takwas a duk fadin Amurka, domin ilmantar da ma’aikatansa kan illolin nuna wariyar launin fata.

Wannan wani mataki ne da kamfanin na Starbucks ya ce zai dauka domin kare aukuwar halayen nuna wariya.

Wannan sanarwar na zuwa ne kwanaki kadan bayan da aka kama wasu maza Amurkawa babaken fata a ciki shagon, wadanda suka zauna a cikin shagon Starbucks da ke Birnin Phildelphia.

Nau’rar daukan hoton bidiyo ta dauki wannan kame, lamarin da ya karade kafofin sada zumunta, ya kuma haifar da bore tare da kauracewa shagunan kamfanin na Starbucks, wanda ya yi fice wajen sayar da shayin gahawa ko kuma Coffee.

Mai magana da yawun kamfanin Camille Hymes ta ce “muna iya bakin kokarinmu a kowace rana domin mu ga mun samar da yanayi da zai yi lale marhabin da kowa da kowa, mun san cewa akwai jan aiki a gabanmu, wannan lamari ya bakanta min rai matuka, ina kuma mai da-na-sanin aukuwar wannan lamari.”

Daga baya dai an saki mutanen biyu, saboda rashin wata hujja da ta nuna cewa sun aikata ba daidai ba.