Ramson-G: Sana'ar Waka Ba Ta Mutanen Banza Bane

Rabson-G

Rabiu Rapson, wanda aka fi sani da Rapson-G mawakin hip-hop da nanaye ya ce ya faro harkar waka da rubutu ne sakamakon, da fari ya ji tsoron kada ya fara waka iyayensa su ki amincewa da sana’ar da ya zabawa kansa, duba da yadda ake kallon masu harkar waka.

Ya ce a kan haka ne ya faro da rubutu, kuma ya lura da cewar idan ya sayarwa 'yan fim zai fi samun karbuwa domin akan samu wasu fina-finan da suke sanya waka a fim dinsu.

Rapson-G ya ce sai wata rana Allah ya hada shi da wani da ake cewa, Danlamin Kima wanda shine ya fara sauraron wakarsa har ya bashi shawarar cewar masu shirya fina-finai zasu karbi wakarsa.

Hakan yasa shi wakar hip-hop da rap kuma yakan waiwayi dabi’ar nan da ke ciwa al'umma tuwo a kwarya, barace-barace da tada husuma da ke fama dasu a Arewancin Nijeriya.

Yana kara jan hankalin matasa masu shawa’awar waka kada su dauki waka ita kadai a matsayin sana’a, ba tare da suna da wata sana’a da zasu iya dogara da ita ba, har sai sun tabbata wannan waka zata iya taimaka musu sus tsaya kan kafafunsu.

Rapson-G ya ce ya lura almajirai sunyi yawa a Nijeriya, da shiga wani yanayi na rashin zaman lafiya da matsalolin talauci da ke addabar mutane.

Your browser doesn’t support HTML5

Sana'ar Waka Bata Mutanen Banza Bane 2' 40"