Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adam Zango Ya Nemi Afuwar Ali Nuhu


Adam A. Zango da Ali Nuhu
Adam A. Zango da Ali Nuhu

A ‘yan kwanakin nan, Adam Zango ya wallafa wasu sakonni makamantan wannan, inda a farkon makon nan ya rubuta wasu kalamai da ke nuni da cewa ya gane “munafukai” ne suke hada su fada.

A wani lamari da babu wanda ya zata, fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya nemi afuwar abokin sana’arsa Ali Nuhu, kan abin da ake gani na da nasaba da rashin jituwar da ke tsakaninsu.

Zango wanda ya yi fice a fannin wake-wake, ya wallafa hotonsa da na Ali Nuhu a shafinsa na Instagram (adam_a_zango), yana tsugune a gefen Ali Nuhu.

“Tuba na ke Sarki….. Gwiwowina a kasa.” Adam Zango ya rubuta da manyan harrufa a karkashin hoton, wanda yake dauke da Ali Nuhu a zaune a kan wata kujera kamar ta sarauta.

Tuni ma’abota finan-finan Hausa suka dunguma zuwa shafin na Zango suna jinjina mai kan wannan rubutu da ya yi.

Ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan labari, mutum 457 suka yi tsokaci kan rubutun na Zango.

“Gaskiya wallahi, wallahi, wallahi…. Ka burge ni sosai wallahi.” Inji ibrahimhamza248.

“Masha Allah, Allah ya kr (kara) hada kanku.” Inji zaytunarh_official.

Zaman doya da manja da jaruman ke yi a dandalin shirya fina-finai na Kannywood ba sabon lamari ba ne ga masu bibiyan harkokin fina-finan Hausa.

A ‘yan kwanakin nan, Adam Zango ya wallafa wasu sakonni makamantan wannan, inda a farkon makon nan ya rubuta wasu kalamai da ke nuni da cewa ya gane “munafukai” ne suke hada su fada.

“Karshen munafukai….. mai wuri ya dawo…..!! Allah ina godiya da irin wannan jarabtar (da) ka yi min….” Inji Zango.

A kuma karshen makon da ya gabata, Zango ya sake aikewa (reposting) da wani hoton bidiyo da Ali Nuhu ya lashe lambar yabo da ya samu kan fim din Mansoor da ya shirya a taron karrama jarumai na AMVC, yana mai taya shi murna.

Kuma Ali Nuhun ya mai godiya kan hakan

“Ina taya Sarkin Kannywood murna.” Inji Zango wanda ya yi rubutu da harshen ingilishi

“Na gode kwarai Prince.” Ali Nuhu ya amsa da inkiyar da ake kiran Zango ta “Prince.”

A baya, an sha sasanta jaruman biyu, wadanda babu wanda ya fi su karbuwa a fannin na shirya fina-finan Hausa.

Amma wani abu da masu lura da al’amura suka yi nuni da shi, shi ne, jaruman ba su taba yin fito-na-fito sun jefawa juna kalamai na batanci a kowanne irin dandalin sada zumunta ba.

Sai dai, magoya baya da wasu makusantansu kan yi ta jefa kalamai marasa dadi akansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG