Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka wato CAF, ta bayyana fushinta tare da mai da martani kan kalaman shugaban kungiyar Napoli ta kasar Italiya Aurelio De Laurentis dangane da gasar kwallon kafar cin Kofin Nahiyar Afirka.
A wata hira da manema labarai a makon jiya, De Laurentis ya kushe ‘yan wasan nahiyar Afirka, yana mai cewa ba zai kuma sayen da ‘yan wasan na Afirka ba har sai sun amince da yarjejeniyar ba za su je buga gasar cin kofin nahiyar ta Afirka ba.
Kungiyar ta Napoli ta yi rashin ‘yan wasanta 2 na ‘yan wasu wasanni, Kalidou Koulibaly dan kasar Senegal da a yanzu ya koma Chelsea, da kuma Andre Zambo Anguissa na kasar Kamaru, sa’adda suka tafi domin wakiltar kasashen na su a gasar ta cin kofin nahiyar Afirka da ta gabata.
To sai dai a wata sanarwa da ta fitar a yau Litinin, hukumar ta CAF, ta bayyana kalaman shugaban na Napoli a zaman rashin mutuntawa ga gasar ta nahiyar Afirka, wadda ta ce ba zai iya yi ba ga ‘yan wasan wasu nahiyoyi kamar Turai, Asia da sauransu, wadanda su ma sukan je domin wakiltar kasashensu a wasu wasanni.
Akan haka CAF ta nemi hukumar kwallon kafar Turai wato UEFA, da ta gaggauta yin bincike tare da ladabtar da De Laurentis, bisa wadannan kalaman.
Tsohon shahararren dan wasan kungiyar Manchester United ta kasar Ingila Wayne Rooney, ya yi kira ga kungiyar da ta gaggauta bai wa Cristiano Ronaldo damar barin kungiyar, idan har abin da yake bukata ke nan.
Kalaman na Rooney na zuwa ne kwana daya bayan da kungiyar ta soma sabuwar kakar wasanni da shan kashi, sa’adda Brighton ta bi ta har a gidanta na Old Trafford, ta doke ta da ci 2-1, a wasan farko ta bude gasar Premier ta bana, duk kuwa da shirye-shiryen da kungiyar ta ce ta yi a karkashin sabon kocinta, domin kawo sauyi a wannan sabuwar kakar wasanni.
Tun a cikin watan da ya gabata Ronaldo ya fito karara ya bayyana bukatarsa ta barin kungiyar inda har aka ta’allaka shi da koma wa wasu kungiyoyi, to amma kuma sabon kocin Eric Ten Hag ya ce ba zai tafi ba, domin yana a cikin sabon tsarinsa.
To sai dai Rooney ya bayyana ra’ayin cewa ba wai Ronaldo baya son wasa a karkashin sabon kocin ba ne, sai dai kuma tun da ya bukaci barin kungiyar, ta yiwu ya kasa sukunin tabuka abin a zo a gani, a daidai lokacin da kungiyar take kokarin gina kakkarfan tubalin ci gaba a wannan kakar wasanni.
Rahotanni daga kasar Spain na bayyana cewa kungiyar Barcelona na duba yiwuwar sayar da dan kasar Gabon Pierre-Emeric Aubameyang, watanni 7 kacal da komawarsa kungiyar daga Arsenal ta Ingila.
Tun bayan da Barcelonar ta cefano Robert Lewandowski daga Bayern Munich ta kasar Jamus, take ganin cewa ya kamata ta rage wasu ‘yan wasan ta na gaba, domin rage tankiya a bagiren, ciki har da shi Aubameyang, wanda kuma tuni aka soma ta’allakashi da komawa Chelsea ta Ingila.
To sai dai kuma wasu rahotanni na bayyana cewa kocin kungiyar Xabi Hernandez, ba ya bukatar rabuwa da dan wasan.
Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk Sanyinna:
Your browser doesn’t support HTML5