Biyo bayan yadda Muryar Amurka ta gudanar da taro don zantawa a kan kalubalen sace yara, wasu iyayen yara da su ka kawo rahoton an sace 'ya'yansu, sun taru a Kano don bukatar hukumomi da sauran jama'a su taimaka wajen gano yaran.
In za a tuna bayan nasarar ceto yara 9 da 'yan sanda suka yi wadanda yawanci a ka sayar da su a Anaca jihar Anambra, wasu iyaye sun kawo rahoton cewa an sace masu yara 49.
Iyayen dai sun bukaci a tsananta bincike don kubutar da 'yaran da su ke sa ran su na raye, wadanda a baya su ka zaci ko matsafa ne su ka sace su don ayyukan tsafi.
Daya daga iyayen al'umma a Kano, Sheikh Abdulwahab Abdallah, ya bukaci babban Sufeton 'yan sanda ya bullo da wani sashe ko runduna domin gano yaran da aka sace.
Ga rahoto a sauti daga wakilin Muryar Amurka Sale Shehu Ashaka.
Your browser doesn’t support HTML5