Rahama Sadau Ta Lashe Lambar Yabo Ta Gwarzuwar Jaruma A Afirka

Rahama Sadau

“A lokacin da aka zabe ni a matsayin wadanda za su kara a neman wannan lambar yabo, na fadawa kaina cewa zan yi alfahari da kaina ko a nan aka tsaya. Ashe ba san cewa ni ce ma zan lashe lambar yabon ba.” In ji Rahama.

Jaruma Rahama Sadau ta lashe lambar yabo ta jarumar da ta fi iya wasan kwaikwayo a nahiyar Afirka a bikin fina-finan Nollywood da aka yi a Toronto da ke kasar Canada.

Rahama ta wallafa lambar yabon a shafukanta na sada zumunta tana nuna farin cikinta da samun wannan karuwa.

“Na lashe kambar yabo ta jarumar da ta fi kowa a nahiyar Afirka da shirin ‘Almajiri’ a bikin karrama jarumai da aka yi a Toronto na fina-finan Nollywood.

“A lokacin da aka zabe ni a matsayin wadanda za su kara a neman wannan lambar yabo, na fadawa kaina cewa zan yi alfahari da kaina ko a nan aka tsaya. Ashe ba san cewa ni ce ma zan lashe lambar yabon ba.” In ji Rahama.

Shirin ‘Almajiri’ fim ne da ya duba irin halin kunci na rayuwa da yara almajirai suke shiga a Najeriya inda suke gararamba a titi.

Fim din ya tattaro fitattun jarumai daga kudu da arewacin Najeriya, irinsu A. Y., Ali Nuhu, Alexx Ekubo, Kanayo O. Kanayo, Broda Shagi da sauransu.