Na samu gogewa a rayuwa sakamakon gwagwarmaya da nisan zangon karatun da na samu wajen mu’amala da mutane daga sassan duniya da dama, inji Rabi Mustapha Sadiq.
Malama Rabi Mustapha, ta ce a lokacin da ta fara karatunta na gaba da sakadare ta so ta zama lauya a rayuwa, kuma har ta fara karatun a kwalejin Aminu Kano, inda ta sami diplomarta, daga nan ne ta nemi cigaba a jami’ar Bayero ta Kano.
Ta ce hakarta bata cimma ruwa ba kasancewar bata samu adadin makin da suke nema ba, ta dalilin haka ne makarantar ta bata wani kwas daban wato na ‘ilimin siyasa wanda aka fi sani da Public Policy and administration”.
Ta kara da cewa bayan ta kamala karatunta ne aka tura ta yi wa kasa hidimi a wani gidan rediyo, bayan kammalawarta ne kuma ta samu gurbin aikin a inda ta yi wa kasa hidima.
Rabi ta ce ko da yake ta fuskanci kalubale da dama a wurin aikinta da ma lokacin da take karatu, amma ta yi kira ga sauran mata da su mike kuma su kasance masu kwarin gwiwa da jajircewa akan duk irin aikin da suka mayar da hankali akai.
Your browser doesn’t support HTML5