Raba Mukamai Ya Tada Jijiyoyin Wuya a Taraba

PDP itace jam'iyyar gwamnan jihar Taraba

Bayan ya zabi mashawarta da hadimai 112 gwamnan jiar Taraba ya sake mika sunayen mutane 20 ga majalisar dokokin jihar da zai nada kwamishanoninsa.

Darius Ishaku na jam'iyyar PDP shi ne gwamnan jihar ta Taraba.

A zabin da ya yi a wata karamar hukumar kusan mutane uku ne ya zaba lamarin da su kansu 'yan PDP basu amince dashi ba. A wasu kananan hukumomi 16 ba haka zancen yake ba.

Rabon mukaman ya harzuka wasu 'yan jam'iyyar PDP da wasu 'yan siyasa dake zargin an nuna wariya da son kai..

Wani Onarebul Abatcha wanda ya yi takara a karkahin PDP yace gwamnan bai yi adalci ba. Da suna tunanen zai hada kawunan 'yan jihar amma sai gashi yana nuna wariya. Ya yi misali da yankin Wukari da rarrabuwar kawuna da ya addabesu inda cikin mutane ukun da gwamnan ya zaba a yankin Wukari bai ba musulmi ko daya ba. Cikin kwamishanoni 20 shida ne kawai musulmai.

Amma yayinda wasu ke kokawa wasu kuma na ganin ba haka zancen yake ba. Alhaji Kyauta Shehu Lau wani kusa a jam'iyyar PDP na ganin yarpiya ce 'yan siyasa ke son yiwa gwamnan.

Yace a sha'anin siyasa ba a yi masa sauri domin kada a fadi. Yace yanzu aka fara nade-nade ba'a gama ba. Wadanda suke korafin ba'a basu ba wai domin su Hausa/Fulani ne sun yi babban kuskure. Wanda yace shi Hausa/Fulani ne a Lau karya ya yi.

Shi ma hadimin gwamnan Alhaji Abubakar Bawa yace cancanta da yawan kuri'u ne aka bi aka raba mukaman. Yace Wukari ta basu kuri'u 60,000 wata karamar hukumar kuma 10 ko 16 ta basu, babu yadda za'a raba mukami daidai da ita. Yace kowa za'a bashi daidai abun da ya yi.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Raba Mukamai a Jihar Taraba Ya Tada Jijiyoyin Wuya - 3' 26"