Ra'ayoyin 'yan Najeriya na karo da juna akan irin hanyar da aka bi har mayakan Boko Haram suka dawo da 'yan matan makaranta dake Dapchi da suka sace.
Batun biyan kudin fansa na ci gaba da jan hankalin jama'a. Akan wannan lamarin kakakin fadar shugaban Najeriya Malam Garba Shehu, ya musanta batun an biya kudi, ko musayar 'yan Boko Hara da ake tsare da su.
A cewar Malam Garba Shehu lokacin da kungiyar ta sace malamai an nuna masu hakan bai dace ba. Da suka sace 'yan matan, masu shiga tsakanin sun sake nuna masu abun da suka yi kuskure ne, su kuma sun yadda akan kuskure suka yi. Ya ce da kansu suka dawo da 'yan matan Inji shi, saboda haka batun bayar da kudi, ko musaya da wadanda ake tsare dasu bai ma taso ba.
Amma har yanzu wasu 'yan Najeriya basu gamsu da irin wadannan bayanai daga irin su Garba Shehu ba. Wani ya ce jaridar Sahara ta ruwaito cewa kudin Euro miliyan biyar, Euro 5m, gwamnatin Buhari ta bayar kafin aka sako 'yan matan. Idan haka za'a rika yi a ra'ayin wasu, yakamata dakarun kasar su dawo daga fafatawa da suke yi da 'yan Boko Haram.
Masanin harkokin tsaro, malam Kabiru Adamu, ya ce, bata yiwuwa 'yan ta'adda su sace dalibai masu yawa, sannan daga baya kuma su mayar dasu haka hannu banza. Ya nemi sanin dalilin da ya sa suka kama yaran, da kuma dalilin da ya sa suka sakosu. Yace gwamnati ta nemi sulhu ne saboda dalili na siyasa saboda zabe ya karato. Su ma 'yan ta'addan suna da dalilai da dama, walau na samun kudi ko samun a sako nasu 'yan kungiyar .
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5