A jiya ne shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da jawabinsa kan halin da kasar Amurka ke ciki, inda ya tabo batutuwa masu yawa da suka hada da na bakin haure da tattalin arziki da siyasa da dimokaradiyya.
Haka kuma ya tabo batun kariyar Iyaka, wanda ya nemi a gina Katanga akan iyakar Amurka da Mexico, lamarin da ‘yan jam’iyyar Democrats suka ki amincewa da shi.
Da suke mayar da martani ga jawabin Trump, ‘yan Najeriya na ganin jawabin ba Amurka kadai ya shafa ba, kasancewar Amurka na zaman tushen dimokaradiyya ga duniya.
Haka kuma ‘yan Najeriyar na ganin cewa batun gina Katanga da Trump ke shirin yi a kan iyakar Amurka da Mexico, na zaman alama ta nuna kyama ga baki, haka kuma ya kamata shugabannin duniya su mayar da hankali wajen kyautatawa al’umominsu domin a daina samun kwararar bakin haure.
Shima wani dan Najeriya da wakilin Muryar Amurka ya zanta da shi a Legas, ya ce jawabin shugaban tamkar mayar da hannun agogo baya a tsarin dimokaradiyya, idan aka duba kudurorinsa irin su gina Katanga da kuma fadan da yake yi da wasu ‘yan Majalisun jam’iyyar adawa.
Domin karin bayani saurari ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya game da jawabin shugaban Amurka Donald Trump.
Your browser doesn’t support HTML5