A yau Talata Shugaban Amurka Donald Trump zai yi jawabi ga Amurkawa kan makomar kasar ko State of the Union, a Turance, a karo na biyu, inda wannan karon zai yi tozali da wata sabuwar Majalisar dokokin tarayya mai mata da ‘yan tsirarun jinsi fiye da yadda aka taba gani.
Shugabar Majalisar Wakilai, wadda za ta zauna bayan Trump a lokacin jawabin, ita ce Nancy Pelosi, wadda ta hada kan ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar Democrat karkashin tuta guda ta yin matukar adawa da batun samar da kudin gina katanga.
Wannan lamari shi ya haifar da rufe wasu ma’aikatun gwamnatin Amurka na lokaci mafi tsawo a tarihin kasar.
Trump zai yi jawabin ne mako guda bayan ranar 29 ga watan Janairu da ya kamata ya yi, wato lokacin da Pelosi ta taka mar birki da cewa jawabin bai yiwuwa har sai an kawo karshen rufe ma’aikatun gwamnatin.
Facebook Forum