Ra’ayoyin Masana Shari’a Game Da Hukuncin Majalisar Dattawan Najeriya

Ginin Majalisa

Masana harkokin shari’a da dokokin kasa na ci gaba da bayyana ra’ayi dangane da kin tabbatar da Ibrahim Magu ya zama shugaban hukumar EFCC da kuma takaddamar da ke wakana tsakanin Majalisar da shugaban hukumar kwastam ta kasar Kanal Hamid Ali mai ritaya.

Tun farkon makon nan wadannan tagwayen batutuwa dai sune suka mamaye jaridun Najeriya, wnnan dai shine karo na biyu da Majalisar Dattawan Najeriya ta ‘ki tabbatar da kujerar shugabancin hukumar EFCC ga Ibrahim Magu.

Lauya mai zaman kansa, Nasiru Adamu Aliyu, ya ce ba yanda za a yi mutanen Najeriya su zabi ‘yan Majalisu da za sau wakilce su, kuma a ce basu da idon da za su kalli abu da idan basira ba, haka kuma ba kan kansu kadai sukayi wannan aiki ba, hukumar tsaro ta fito ta bayyana cewa Magu bashi da ‘kima da zai shugabanci hukumar yaki da cin hanci da rashawa. sai dai kuma babu wanda ya fito ya ce tuhumar da ake wa Magu ba gaskiya bane.

Shi kuma Barista Abdu Bulama, tsokaci ya yi dangane da takaddamar da ke wakana tsakanin Majalisar Dattawan Najeriya da shugaban hukumar kwastam kanal Hamid Ali. Inda yace tsarin mulki ya baiwa Majalisa damar gayyatar duk wanda suke so a Najeriya. A cewar Bulama idan har Hamid Ali zai rike mukamin to bai kamata ba ya raina rigar da masu mukamin ke sawa ba.

Don cikakken bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Ra’ayoyin Masana Shari’a Game Da Hukuncin Majalisar Dattawan Najeriya - 3'31"