Shugaban ya ce kudaden na cikin rarar da aka samo daga kungiyar Paris Club da ta mayarwa Najeriya saboda ta biya fiye da bashin da kungiyar ke binta.
To sai dai yayin da ake shirin raba masu kudaden akwai wasu sama da Naira biliyan uku da ake zargin wasu gwamnoni da rashin bin ka'ida da tsare-tsaren da aka ba su na yadda za su yi amfani da kason farko.
Sabanin haka sun yi abun da suka ga dama da kudaden ko da yake gwamnati ba ta bayyana sunayen jihohin da suka yi gaban kansu da kudin ba.
A yanzu shugaban na fatan za'a bi ka'ida a wannan karon, inda ya yi a garesu da su yi abin da ya kamata.
Domin jin karin bayani kan wannan batu, saurari abin da kakakin shugaban kasan Malam Garba Shehu ya ce a wannan rahoto da Umar Faruk Musa ya hada.
Facebook Forum