A ranar Talata ne, Babban kotu a Abuja ta yankewa Dariye shekaru biyu kan almubazaranci da dukiyar al'umma da kuma wasu shekaru 14 kan laifin rashin rikon amana. Hukumar yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon kasa wato EFCC ce ta gurfanar da Dariye kan zargin wawure kudade Naira biliyan 1.1 da aka bai wa jihohi masu fama da matsalar zaizayar kasa.
Dariye wanda a yanzu haka shine Sanata mai wakiltar Filato ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, ya maido da Naira miliyan 550, yayin da Naira miliyan 660 ba su babu dalilinsu.
Wasu na ganin hukuncin da kotu ta yanke yayi daidai domin hukunta wadanda ake samu sun zalunci al'umma ta hanyar yin sama da fadi da dukiyoyinsu.
"Duk wanda ke da hannu cikin zalunci a cikin wannan kasa, idan shari'a za ta bi ta kamoshi a gurfanar da shi gaban hukuma a kuma yanke mai hukunci na gaskiya, to muna goyon bayan wannan." inji wani dan jihar Filato
Ya kuma kara da cewa,
"Duk wanda ke da hannu a cikin halin da muka tsinci kanmu yau, ina tabbatar da cewa idan har shari'a za ta bi ta kamosu, to kasar za ta gyaru."
Sai dai wasu sun nuna rashin jin dadi da wannan hukunci.
"A matsayina na dan jihar Filato, na ji tausayinsa sosai domin na ga azaban da ya sha tun 2004, inda aka cireshi ba bisa ka'ida ba, ya dawo da kyar ya karasa, yanzu kuma ya sake komawa sai ga wannan ya faru, saboda dan kurakuran da aka sameshi da shi."
Saurari rohoton Zainab Babaji
Your browser doesn’t support HTML5