Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'a Sun Gamsu Da Shirin Kafa Sabuwar Kasuwar Gwari a Jihar Imo


Sabuwar kasuwar kayan gwari za ta taimaka wajen habbaka kasuwanci a jihar Imo.
Sabuwar kasuwar kayan gwari za ta taimaka wajen habbaka kasuwanci a jihar Imo.

Gwamnatin Jihar Imo tare da hadin gwiwar wasu Hausawa mazauna jihar na kokarin kammala aikin wata kasuwar kayan gwari a garin Okigwe

Shugaban karamar hukumar Okigwe, Mr. Beneth Eliochine ya ce wannan yunkurin babban ci gaba ne ga jihar da kuma sauran ‘yan kasuwa da suka fito daga sauran sassan kasar.

Kasuwar za ta taimaka wajen samar da aikin yi ga matasa, kana za ta kawo ci gaban kasuwanci tsakanin al’ummar yanki Arewa da na kudu, kuma kasuwace da za ta taimaka matuka wajen ganin an tsaftace muhalli.

Shugaban kungiyar dillalan kayan gwari,Mallam Shugaba Mika’ilu Kigani ya bayyana jin dadinsu da wannan kasuwar, domin zai sa masu sana’ar gwari su dawo kasuwar da zarar an kammala aikinta. Sannan suna kira da jama’ar Arewa masu hannu da shuni da su taimaka musu wajen ganin an kammala gina kasuwar cikin karamin lokaci.

Shi ma Shugaban al’ummar Arewa mazauna jihar ta Imo, Alh. Abdullahi Yaya Biu ya bayyana gamsuwarsa da kasuwar, inda ya ce suna sa ran za ta samar da kyakkyawar dangantakar kasuwanci tsakanin Arewa da kudancin kasar da kuma ci gaban tattalin arzikin kasar Najeriya ba wai jihar kadai ba.

Domin samun karin bayani sai a saurari rahoton Alphonsus Okoroigwe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG