A Talatar data gabata ne a yayin zaman hadin gwiwa tsakanin majalisar wakila data dattawa, ‘yan majalisar kasar suka zartar da wasu kudirori 12 dangane da halin da kasar ke ciki.
Kudurorin sun kunshi batutuwan tsaro, da na tattalin arziki da kalubalen rashin aikin yi tsakanin ‘yan kasa da zargin rashin mutunta dokokin tafiyar da harkokin gwamnati akan wasu mutane da shugaba Buhari ya nada kana da kuma muzgunawa ‘yan hamayya da wadanda ba sa goyon bayan gwamnati.
Masu kula da lamara dai na cewa, wannan mataki na majalisar dokoki ta Najeriya na kara fito da halin rashin jituwa daya dade yana wakana tsakanin majalisar da gwamnati kuma babbar barazana ce ga sha’anin dimokradiya
Dr Abbati Bako masanin kimiyyar siyasa a nan Kano y ace abubuwa kwatankwacin hakan sun faru a wasu kasashe. Hakan ya faru a Nijar an san abun da ya faru. Idan an ci gaba da sa-in-sa tsakanin ‘yan majalisa da bangaren zartaswa Dimokradiya zata gurgunce, kasar kuma ta fada cikin wani hadari. Ya kira ‘yan siyasar kasar da su yi taka tsantsan.
Shi-ma Comrade Nura Iro Ma’aji babban jami’N a kungiyar CISLAC mai rajin tabbatar da demokaradiyya a najeriya na cewa abubuwan dake faruwa tsakanin bangarorin biyu basu ba su mamaki ba. ‘Yan majalisa ba mutanen kasar suka sag aba ba. Shugaban kasa ne kawai ya damu da ‘yan kasar. Amma ya yi kira ga shugaban kasa ya sabunta alaka da ‘yan majalisa domin a warware takaddamar dake tsakaninsu. Y ace ba dede ba ne shugaban kasa ya bar wasu a cikin fadarsa suna anfani da wani bangaren gwamnati suna rigima da shugabancin majalisa bai dace ba.
Yanzu haka dai majalisar dokokin ta Najeriya ta sha alwashin rubuta wasika ga majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayyar turai da kungiyar majalisun dokoki renon iIngila da sauran kungiyoyi da cibiyoyin demokaradiyya a duniya game da abin da suka kira halin ni’yasu da demokaradiyyar Najeriya ta shiga. Dr Abbati Bako ya yi karin haske.
Inda yake cewa ‘yan majalisar zasu rubuta wasikar da sha alwashin rubutawa ne saboda sun san suna da ruwa da tsaki ne akan tafiyar da Dimokradiya. Amma “idan wanna ya faru za’a fara yiwa Najeriya dariya a yadda muke tafiyar da dimokradiyarmu”
Majalisar dai tace muddin shugaba Buhari bai dauki matakan da suka dace ba game da kudurorin data cimma, babu shakka ita kuma a nata bangaren zata dauki matakin daya kamata dai-dai da tanadin dokokin kasa.
A saurari rahoton Mahmud IbrahimKwari da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5