Ra'ayin Jamhuriyar Nijer Kan Burkina Faso

Isaac Zida da Zephirin Diabre a Ouagadougou, Burkina Faso, Nuwamba 2, 2014.

A karin farko da gwamnatin kasar jamhuriyar Nijer ta bayyana ra’ayinta kan abinda ke faruwa a makwabciyar kasar Burkina Faso.

A wata hira da wakilin Muryar Amurka yayi da Ministan harkokin wajen kasar ta Nijer Bazum Muhammed, ya shaidawa Abdoulaye Mamane Amadou cewar muddin soja ya nace zai jagoranci kasar ta Burkina Faso, kungiyoyi kamar ECOWAS zasu dauki matakai akan kasar saboda hakan su shirya kansu tun daga yau.

Saurari wannan rahoton aji hirar.

Your browser doesn’t support HTML5

Ra'ayin Nijer Kan Burkina Faso - 3'56"