Mai Shari’a Anthony Kennedy da sauran alkalai masu raayin rikau sun bayyana tababar su akan wannan karar da iyayen wannan yaro zasu iya shigarwa, yayin da su kuma wasu alkalan 4 masu ra’ayin sassauci suka nuna goyon bayan su akan yiyuwar hakan, domin ko hujjar su ita ce wannan harbin da akayi a cikin shekarar 2010 ya faru ne a kusa da kan iyakar kasashen biyu wanda kuma kasashen ke daukar alhakin kula da su.
Wato sun rabu 4-4, don haka zasu bar hukuncin karammar kotun Kenan wadda ta tayi watsi da wannan karar da iyayen wannan yaron suka shigar akan jami’in na Amurka, mai suna Jesus Mesa.
To sai dai kotun na iya kawo wa shara’ar tsaiko tunda an samu ra’ayi daidai-wa-daida ne, har sai majalisar Dattijai ta tabbatar da nadin babban alkalin alkalai na kasa, Neil Gorsuch wanda zai iya jefa kuria’ar karshe domin sanin matakin da za a dauka game da wannan batu.
Idan anyi haka to zai baiwa kotun koli damar sauraren karar.