Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Sun Yi Zanga-zangar Kin Jinin Trump


masu zanga-zanga
masu zanga-zanga

Dubban masu zanga-zanga sun yi gangami a fadin kasar Amurka na bayyana rashin amincewarsu da gwamnatin Donald Trump a jiya Litini, wadda ita ce zagayowar Ranar Tunawa da Shugaban Amurka na farko.

Gangamin, mai taken "Ba Shugaban Kasa Ta Ba Ne" ya taro masu zanga-zanga da dama daga fadin kasa, wadanda su ka fito su na nuna goyon baya ga tsirarun jinsuna, da baki da Musulmi da ma'aikata da 'yan luwadi da madugo da masu canza jinsi da kuma matalauta.

An gudanar da zanga-zanga kama daga birnin Boston zuwa Seattle, inda masu zanga-zangar su ka ce niyyarsu ita ce su mai da ranar ta zama ta nuna bijirewa ga manufofin Trump.

A birnin New York, dubban masu zanga-zanga sun mamaye file mai cin manyan gine-gine har 8 daura da otal din Trump na kasa da kasa. Masu gudanar da zanga-zangar sun fadi a kafar FaceBook cewa, "Donald Trump shugabanmu ne amma na jeka-na-yi-ka, ya na adawa da duk wata dabi'ar da mu mutanen New York mu ka amince da ita, kuma bai kare muradunmu."

Mutane da dama sun taru a birnin Washington, su na ta ihu "A a yi watsi da Trump."

A birnin Chicago ma daruruwan mutane sun taru daura da ginin Trump Tower, su na rike da sakonni da harsunan Turanci da Larabci da kuma Sifaniyanci, su na kiran da a bijere ma manufofin Trump game da baki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG